Azumin 2026: Hon. Ɗayyabu Ladan Ya Ciƙa Muraden Al’ummar Ganjuwa Ta Gabas Ta Hanyar Kyakkyawan Wakilci

 A daidai lokacin da shugabannin da suke bai wa magance matsalolin al’umma muhimmanci suke wahalar samu, wani ɗan majalisa ya yi fice ta hanyar wakilci mai armashi bisa bukatun jama’a. A wannan wata mai alfarma na Ramadan wanda ake ninka ladan ayyukan alheri, Hon. Ɗayyabu Ladan Mohammed, ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Ganjuwa ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, ya ɗauki matakai domin tallafa wa al’ummarsa.

Ɗan majalisar ya yi amfani da wannan dama domin sauƙaƙa wa rayuwar al’ummar da yake wakilta, tare da sanya farin ciki a zukatansu da kuma tabbatar da cewa har yanzu akwai shugabanni nagari.

A yayin shirin rabon tallafin, ya raba kayayyakin azumi da kuma kuɗaɗe ga al’ummar da suka fito daga gundumomi daban-daban da suka ƙunshi mazaɓar Ganjuwa ta Gabas.



Al’ummar yankin sun bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko ba, domin Hon. Ɗayyabu Ladan ya shahara wajen kawo romon dimokuraɗiyya a sassa daban-daban na mazaɓarsa.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da shaddodi 200, zannuwa 200, manyan riguna 50, sannan kuma kuɗi kimanin Naira Miliyan Goma Sha Biyu da Dubu Ɗari Biyar (₦12,500,000).

Waɗanda suka amfana sun haɗa da matasa, mata, dattijai, shugabannin al’umma, malaman addini, mambobin ƙungiyoyi, jigajigan jam’iyya da kuma masu ruwa da tsaki a yankin.

Taron rabon tallafin ya samu halartar Shugaban Ƙaramar Hukumar Ganjuwa, Hon. Idris Magayaki, shugabannin jam’iyyar PDP na yankin, ƴan siyasa, ƙungiyoyin mata da matasa, da sauran jama’a.

Mutane da dama sun bayyana cewa irin wannan tallafi na da matuƙar muhimmanci musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki. Sun ƙara da cewa Hon. Ɗayyabu Ladan na ci gaba da zama abin koyi ga sauran shugabanni wajen samar da ci gaba ga al’umma.

✍️ Mukhtar Garba Kobi

8/2/2026

Comments