KAKAKIN MAJALISAR DOKOKIN TA JIHAR BAUCHI YA WADATAR DA RUWAN SHA GA AL'UMMAR MAZAƁARSA



  Ruwa ya kasance wani ginshiƙi ne na wanzuwar al'umma wanda rayuwa dole sai dashi, rashinsa ko ƙarancinsa ke haddada tagayyara, fari da kuma ci baya ga tattalin arziki. Sanin waɗannan dalilai suka sanya mai girma Kakaki Majalisar Dokoki Ta Jihar Bauchi kuma memba dake wakiltar mazabar Ningi Ta Tsakiya, Rt. Hon. Dr. Abubakar Y Suleiman (Dangaladiman Ningi) ya gudanar da ayyukan tonon famfunan burtsatsai domin amfanar da al'ummar mazaɓarsa.


  Kafin gudanar da ayyukan, sai da aka nazarci yankunan tare da binciko wurare masu tsananin buƙatar ruwa, ƙwararru suka yi ayyukan gano inda ke ɗauke da mamakon ruwa hakan ya bada damar fara ayyukan. An tona famfunan burtsatsen ne da zummar kawo ƙarshen shafe nisan zango don neman ruwa, sauƙaƙawa domin buƙatun dubban jama'a, dabbobi har ma da masu ayyukan noman rani.


  Binciken sirri tare da magance matsalolin da suke addabar al'ummarsa suna daga cikin ɗabi'un ƙwarai na Ɗangaladiman Ningi babu shakka al'ummar Ningi ta tsakiya suna sharbar romon dimokradiyya sakamakon wakilcin jagora mai son kawo cigaba. Wuraren da akayi ayyukan tonon famfunan sun haɗa da Ɓaure Ari ward, Unguwar Gwarina dake Tiffi, Gadar Maiwa Unguwar Fulani, Gardo Fulani dake Nasaru B sai Fanisau.


  Sauran sune Tudun Alƙali dake Tiffi, Bagare Hayin Mai Doki, Sabuwar Tiffi, Kafin Zaki, Ari Jama'a sai na ƙarshe a Dingis. Dukkan waɗannan yankuna tuni sun fara cin gajiyar wakilci nagari na Kakakin wanda ya yaye ƙuncin rashin ruwa. Jama'a da dama sun nuna farin cikinsu tare da godiya ga Rt. Hon. Dr. Abubakar Y. Suleiman bisa ayyuka a fannonin ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi, inganta noma, bunƙasa sana'o'i da bayar da jari don kawar da zaman banza.


Daga:

Mukhtar Garba Kobi 

Mai Magana Da Yawun Kakakin Majalisar Dokoki Ta Jihar Bauchi 

18/11/2025

Comments