HON. IBRAHIM TANKO BURRA YA AZA TUBALIN AYYUKAN MILIYOYIN NAIRA DOMIN CI GABAN MAZABARSA

 

A ci gaba da tabbatar da alkawuran da ya ɗauka ga al'ummarsa, ɗan majalisar dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Mazabar Burra, Hon. Ibrahim Tanko Burra, ya kaddamar da wasu manyan ayyukan raya ƙasa da za su sauƙaƙa rayuwar al'umma tare da inganta muhallinsu da tattalin arzikinsu.



A cewar Hon. Ibrahim Tanko Burra, ayyukan sun samo asali ne bayan nazari da tattara bukatu daga gundumomin Bashe, Gamji da Kafin Lemo. Ayyukan dai za su lashe adadin kuɗi har naira miliyan ɗaya da dubu dari huɗu da casa'in da biyu (₦1,492,000). A halin yanzu, wakilin ya riga ya miƙa rabin kuɗin domin fara gina ababen more rayuwa kamar magudanan ruwa, gadoji, fanfunan burtsatse, gyaran masallatai, da kuma rumfunan kwata.


A cikin waɗannan ayyukan, gundumar Agwarmaji ta samu ₦700,000 don aikin magudanar ruwa. Gundumar Gamji kuma ta karɓi ₦250,000 domin gina rumfar kwata, yayin da aikin Bashe ya samu tallafin ₦600,000. Har ila yau, domin cika ƙwaƙƙwaran buƙata daga masallacin Tashan Loko, Hon. Burra ya bayar da gudummawar ₦100,000 don siyan ƙyamare da sauran kayayyakin ibada.


Baya ga hakan, wakilai 26 daga gundumomin da ayyukan za su amfana sun samu kyautar ₦10,000 kowannensu, yayin da kowacce bas ɗin sufuri ta samu tallafin ₦50,000. A dunkule, Hon. Ibrahim Tanko Burra ya fitar da kimanin naira miliyan uku da dubu hamsin (₦3,050,000) a rana guda, domin inganta walwala, sauƙaƙa sufuri da kuma samar da muhallin ibada mai tsafta da kwanciyar hankali.


A martaninsu, Yahaya Ibrahim Lingya daga Bashe, Ado (Shugaban Matasa) daga Gamji, da Usman Galadima daga Agwarmaji sun bayyana matuƙar godiya ga Hon. Ibrahim Tanko Burra bisa ci gaba da jajircewa da ya ke yi wajen kawo sauyi mai ma’ana. Sun kuma sha alwashin kula da tabbatar da ingancin aiki da amfani da kayan aiki masu ɗorewa.

Comments