Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ya Ba Da Tallafin Kuɗi Ga Al’ummar Mazabarsa Ta Ningi

 


Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Dr. Abubakar Y. Suleiman (Dangaladiman Ningi), ya sake nuna kishinsa da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al’ummarsa ta Mazabar Ningi ta Tsakiya, ta hanyar bayar da tallafin kuɗi ga mabukata.


A wata sanarwa da mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar, an bayyana cewa fiye da naira dubu dari bakwai (₦700,000) ne aka bayar a matsayin tallafi don biyan bukatu daban-daban a cikin al’umma. Tallafin da aka bayar a ranar Juma’a ya haɗa da biyan kuɗin magani, kuɗin rajistar makarantu, gudunmawar gina masallaci, da kuma tallafin aure ga ma'aurata masu niyya.


“Wannan taimako alama ce ta shugabanci na gari da ke fifita jin daɗin al’umma fiye da moriyar kai,” in ji sanarwar, wacce ta ƙara da cewa an bai wa waɗanda suka fi bukata ne daga cikin masu karamin karfi da kuma waɗanda ke fuskantar matsin tattalin arziki.


Mabukatan da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da nuna godiyarsu ga Kakakin Majalisar bisa wannan jinkai da kulawa. Sun kuma yi masa addu’ar samun nasara da cika burinsa na hidimtawa al’umma.


Rt. Hon. Dr. Abubakar Y. Suleiman, wanda ke wakiltar Ningi ta Tsakiya a Majalisar, ya sake tabbatar da cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa da kuma kyautata rayuwar al’ummarsa.

Comments