Gwamna Inuwa Yahaya Ya Karɓi Baki Cikin Girma a Bikin Ɗiyar Tsohon Gwamna Dankwambo a Gombe ...Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da Wasu Suna Yabon Gwamnan Gombe Kan Ƙoƙarinsa na Ƙulla Ƙawance Tsakanin Jama’a
A wani gagarumin nunin ƙwarewar siyasa da halin ɗan ƙwarai, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, a yau ya shirya wani babban liyafa don girmama tsohon Gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda ya ba da auren diyarsa, Hafsat.
An gudanar da bikin liyafar ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da ke Gombe, inda manyan baki daga sassan ƙasar nan suka halarta, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai, Gwamnonin jihohin Bauchi da Oyo, ‘yan majalisa daga matakin ƙasa da na jiha, sarakunan gargajiya, masu hannu da shuni da sauran baki daga cikin da wajen jihar.
Masu jawabi a wajen bikin sun yaba da yadda Gwamna Inuwa Yahaya da kansa ya shirya wannan liyafa, suna mai cewa hakan ya nuna nagartaccen shugabanci da ya wuce bambancin jam’iyyu. Sun bayyana cewa wannan ƙoƙari ya ƙara tabbatar da matsayin Gwamnan a matsayin mai haɗa kai da ɗan kishin al’umma, wanda ke da kishin zaman lafiya, girmama juna da haɗin kai.
A sakonsa na fatan alheri, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya nuna godiya ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa tarba da girmamawar da aka nuna wa baki, yana mai cewa hakan ya nuna halin ɗan wasa da karamci wanda ba kasafai ake samu ba a siyasar Najeriya ta zamani.
“Mun gode da yadda kuka karɓe mu da girmamawa saboda ɗaya daga cikinmu. Gombe a karkashin jagorancinku na nuna sahihin fahimta da haɗin kai na siyasa da ya cancanci yabo,” in ji Sanata Akpabio.
Ya ƙara da cewa, “Zuwan Sanatoci sama da bakwai daga jam’iyyu daban-daban a yau, alama ce ta yadda Sanata Dankwambo ke haɗa kan jama’a, kuma shaida ce ga zaman lafiya da karɓar baki a Jihar Gombe.”
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, shima ya bayyana ra’ayinsa da irin wannan yabo, yana mai jinjinawa rawar da Gwamna Inuwa Yahaya ke takawa wajen haɗa kan mutane da kuma darasin haɗin kai da auren kansa ya koyar.
“Wannan aure ne da ya haɗa iyalai daga jam’iyyu daban-daban. Wannan ne abin da Najeriya ke buƙata: haɗin kai tsakanin jam’iyyu, ƙabilu da addinai. Matsayin da Gwamna Inuwa ya ɗauka a wannan bikin ya nuna halinsa da hangen nesansa na ƙasa ɗaya,” in ji Kakakin Majalisar.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a nasa jawabin, ya yaba da Gwamnan, yana mai cewa halin da ya nuna ya fito ne daga zuciya mai cike da tawali’u da goyon bayan jama’a a lokutan farin ciki da na damuwa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko wuri ba.
A jawabin maraba da baki da ya gabatar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana farin cikinsa na karɓar wannan taro, yana mai cewa Gombe ta shahara da zaman lafiya, girmamawa da karɓar baki.
Gwamnan ya yi amfani da damar wajen jaddada muhimmancin haɗin kai, juriya da girmama juna, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan asalin Jihar Gombe.
Ya bayyana cewa duk da bambancin siyasa, ƙabila ko addini, al’ummar Gombe sun kasance ƙasa ɗaya da manufa ɗaya: ta gina al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.
“Mu a Gombe muna da akidar kasancewa al’umma ɗaya. Wannan biki wani haske ne na hakikanin halinmu; masu karɓar juna, masu zaman lafiya, kuma masu haɗin kai. Fatanmu shi ne wannan rana ta ƙarfafa zumunci a tsakanimmu, ba wai a matsayin shugabanni ko abokan aiki kawai ba, amma a matsayin ‘yan uwa da ke da buri ɗaya na ganin Najeriya ta cigaba,” in ji Gwamnan.
A jawabinsa na godiya, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana godiya matuƙa ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa goyon bayansa, zumunci da haɗin kai da ya nuna daga farko har ƙarshen bikin auren.
“Ina godiya ta musamman ga Gwamna Inuwa Yahaya saboda irin goyon bayan da ya ba ni a wannan lokaci mai muhimmanci. Goyon bayansa – da na jiki da na zuciya – ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar wannan bikin. Wannan ne shugabanci na gaskiya da ƙawance na hakika, kuma ina godiya ƙwarai,” in ji Sanata Dankwambo.
An gudanar da ɗaura auren Hafsat da Ashraf ne tun da farko a fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, CFR.
Comments
Post a Comment