Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi ya raba fiye da Naira milyan 2.8 ga yan mazabarsa domin bikin Sallar Layya
Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Rt. Hon. Dr. Abubakar Y. Suleiman (Ɗangaladiman Ningi, Barden Kudun Katagum), ya raba fiye da naira miliyan biyu da dubu dari takwas da biyar (₦2,805,000) ga al’ummar mazabarsa ta Ningi Central domin taya su murnar bikin Babbar Sallah da ke tafe.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar, Kakakin ya bayyana cewa wannan tallafi na kudi na da nufin rage wa jama’a radadin matsin tattalin arziki da kuma taimaka musu wajen gudanar da ibadun Sallah cikin sauki da annashuwa.
Masu cin gajiyar tallafin sun fito ne daga kowane yanki na mazabar Ningi Central, ciki har da matasa, mata, dattijai, shugabannin al’umma, mambobin jam’iyyu da kuma masu amfani da kafafen sada zumunta.
Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman ya shahara wajen bayar da tallafi ga al’umma ba tare da la’akari da jinsi, matsayi ko bambancin siyasa ba. Hakan ne ya sa ya zama abin alfahari da kwatance ga shugabanni da dama.
Yayin da suke karɓar tallafin, mafi yawan wadanda suka amfana sun bayyana farin cikinsu tare da godiya ga Kakakin bisa kulawarsa da yadda yake sanya bukatunsu a gaba fiye da tasa. Sun kuma yi masa addu’ar samun nasara a rayuwa da harkokin siyasa.
Comments
Post a Comment