GWAMNATIN JIHAR GOMBE TA RUSHE GIDAJEN GALA BIYAR 5
A kokarinta na gyaran tarbiyya tare da kawo karshen ayyukan assha, Gwamnatin jihar Gombe ta rushe gidajen Gala da ake aikata masha’a a cikin su a yankunan Tumfure da kuma BCJ dake karamar hukumar Akko.
Wannan na Kun she ne cikin wata sanarwa da Mai taimakawa Gwamnan Gombe na musamman bangaren sadarwa Safiyanu Danladi Mairiga, ya wallafa a shafinshi na fesbuk, inda yace, Shugaban kwamatin rufe gidajen Galan ne Capt (Rtd) Bitrus Bilal ya jagoranci ayyukan rushe-rushen wanda ya gudana a ranar Alhamis dinnan data gabata.
A cewar Bilal gidajen da aka rushe an gina su ne ba bisa ka’ida ba kamar yadda hukumar kula da tsarin birane GOSUPDA ta bayyana. Sa’annan kuma abubuwa da akeyi a gidajen sun saba tsarin doka da kuma al’adun alummar jihar Gombe.
Idan za’a iya tunawa, a satin baya ne Gwamna Inuwa Yahaya ya bada umurnin rufewa tare da rushe duk wani gidan Gala dake fadin jihar saboda kokarin gwamnatin na tabbatar gyaran tarbiya da haramta ayyukan assha a jihar.
Comments
Post a Comment