KYAWAWAN SIFFOFIN SHUGABANCI GUDA 10 NA GWAMNA INUWA YAHAYA




Ba zai yiwu a samu ma'sumin shugaba ba (bayan Annabi). Babu mutumin da ba ya kuskure tunda dukkanmu muna da zalla. Amma nagartaccen shugaba shine wanda alheransa suka ninninka rauninsa. Ga nagartattun siffofi guda 10 na Gwamna Inuwa. 

1. Himma da jajircewa wajen aiki: Dukkan nagartattun shugabanni suna da sifar dagewa da himma a wajen aiki. Ba karamar nasara ba ce ga jiharmu kasancewar mun samu jajirtacce gwamna haziki wanda ba ya gajiya da aiki dare da rana, har ma a kwanakin asabar da lahadi. 

2. Kishin Kasa: Abu ne bayyananne cewa Gwamna Inuwa yana matukar kishin ciyar da Gombe gaba. Ya gayyato manyan kungiyoyi na gida da na waje masu kawo tallafin ayyukan ci gaba, fiye da duk wani gwamna a tarihin Gombe.  

3. Iya Zakulo Kwararru: Dukkan nagartattun shugabanni sun kware wajen iya zakulo kwararru, masanafitattu a harkar gudanarwa wadanda za su cike gurbin duk wata gazawar shugabannin. Danmaje ya yi fice matuka wajen ba da dama ga fitattun manyan ma'aikatan gwamnati da kuma matasa hazikai don bada tsasu gudumawar wajen gida kasa da bunkasa harkokin ilimi, da lafiya, da fadada hanyoyin shigar kudade, da gina kayakin more rayuwa da inganta hanyoyin kashe kudaden jiha, da kuma samar da ingantaccen shugabanci da tsarin gudanarwa. 

4. Dabarun Sarrafa Harkar Kudaden Jiha: Kasancewar Gwamna Inuwa kwararre ne a harkar sarrafa kudi, ya taimaka wajen tabbatar da cewa an alkinta dukkyar jihar, kuma an 

cin ma manyan ayyuka 

da kudade 'yan kadan. Kamar yadda kuma ya toshe hanyoyin barnata dukiyar jiha da hallaka ta. 

5. Hakuri da Juriya: Gwamna Inuwa ya jajirce ya kuma sadaukar da kansa don kawo cigaba, tare da daukar duk wata wahala ko kalubale da ma kashe guiwa da yake foskanta. Ko kadan tubatibai ba su sanya karaya wajen cin ma manufarsa ta bunkasa Gombe ba. Ya tsaya tsayin daka, Ko Gezau, ba sarewa, ba fasawa, babu gudu ba ja da baya wajen aiwatar da ayyukan da ya saka a gaba. 

6. Hangen Nesa: Gwamna Inuwa shugaba ne mai hangen nesa. Tunaninsa ba 'yan yau kadai ba ne. Bai takaita tunaninsa a kan cin zabe ba. A'a! Yana hango alkibla da makomar jiharmu ne da kuma jama'arta ashekaru masu zuwa, ba kawai a iya wa'adin mulkinsa ba. Saboda manufar gina Gombe da sanya ta a kan gwadabin cigaba mai dorewa, ya kan dauki kwararan matakai kuma ya aiwatar da su, ko da kuwa sun kaucewa muradunsa na siyasa.

8. Iya Magance Matsaloli: Gwamna Inuwa ya gwananci wajen warware manyan matsaloli da ke tankarar al'umma. Ta haka ne ya aiwatar da shirin 3G wanda yake magance matsalar zaizayar kasa da habakar kwarurruka ta hanyar dashen miliyoyin bishiyoyi, ya samar da tsarin asusun tallafin lafiya, da inganta makarantun tsangaya a karkashin hukumar BESDA, da sauransu. 

9. Faro Sabbin Dabarun Shugabanci: Kamar yadda kungiyar Gwamnoni ta Progressive Governors Forum ta tabbatar, Gwamna Inuwa fitacce ne a cikin dukkan Gwamnoni wajen kirkiro da samar da sabbin dabarun tafiyar da gwamnati a Najeriya. Shaida a kan haka shine irin hanyoyin gina kasa na musamman da ya faro wadanda suke kawo cigaba na musamman a fadin jihar Gombe.  

10. Sanya Ido da Bibiyan Ayyuka: Gwamna Inuwa yana sanya ido wajen bibiyan ayyukan da ya bayar don tabbatar da cewa an aiwatar dasu. Ya yi tabbataccen tsari na ganawa da tattaunawa da wakilan gwamnati a dukkan bangarori domin tabbatar da ayyuka suna tafiya daidai. 

Hakika, kyawawan siffofin shugabanci na Gwamna Inuwa sun dara kurakurensa. Abun da muke fata shi ne zai gina a kan kyawawan ayyukansa da nagartattun siffofinsa, kuma zai kara kokari wajen magance da gyara wuraren da yake da rauni. 

Da fatan kuma mutanen Gombe za su masa afuwa a kan kurakurensa, su kuma su tuna alheransa masu tarun yawa. 

Inuwa ya yi alheri mun gani. Kada mu yi kuskuren sake reshe mu kama ganye.

Comments

Popular posts from this blog

Shamsudeen Bala Mohammed: A Brilliant Mind, A Generous Heart, and A Life Worth Celebrating

Speaker of Bauchi State House of Assembly Felicitates with Governor Bala and Citizens on Democracy Day

Distinguished Senator Ibrahim Hassan Dankwambo: A Shining Example of Inclusive Leadership