KYAWAWAN SIFFOFIN SHUGABANCI GUDA 10 NA GWAMNA INUWA YAHAYA

Ba zai yiwu a samu ma'sumin shugaba ba (bayan Annabi). Babu mutumin da ba ya kuskure tunda dukkanmu muna da zalla. Amma nagartaccen shugaba shine wanda alheransa suka ninninka rauninsa. Ga nagartattun siffofi guda 10 na Gwamna Inuwa. 1. Himma da jajircewa wajen aiki: Dukkan nagartattun shugabanni suna da sifar dagewa da himma a wajen aiki. Ba karamar nasara ba ce ga jiharmu kasancewar mun samu jajirtacce gwamna haziki wanda ba ya gajiya da aiki dare da rana, har ma a kwanakin asabar da lahadi. 2. Kishin Kasa: Abu ne bayyananne cewa Gwamna Inuwa yana matukar kishin ciyar da Gombe gaba. Ya gayyato manyan kungiyoyi na gida da na waje masu kawo tallafin ayyukan ci gaba, fiye da duk wani gwamna a tarihin Gombe. 3. Iya Zakulo Kwararru: Dukkan nagartattun shugabanni sun kware wajen iya zakulo kwararru, masanafitattu a harkar gudanarwa wadanda za su cike gurbin duk wata gazawar shugabannin. Danmaje ya yi fice matuka wajen ba da dama ga fitattun manyan ma'aikatan gwamnati...